Rage Kudin Manyan Makarantun Gwamnatin Kaduna : Gwamna Uba Ya Cancanci Yabo- ADC Reshen Kaduna

  


Hon. Ahmed Tijjani Mustapha,
Shugaban jami'yyar ADC.Daga Abubakar Abba 


Shugaban jami'yyar ADC reshen jihar Kaduna Hon. Ahmed Tijjani Mustapha, ya yabawa gwamnan jihar Sanata Uba Sani kan hangen nesan na rage kudin manyan makarantu mallakar gwamnatin jihar. 


Yabon na kunshe ne a cikin sanarwar da ya rabawa manema labarai a jihar, inda ya yi nuni da cewa, rage kudin gwamnan ya yi dubi ne akan kokaken da musamman iyaye sukai ta yi a baya kan karin kudin makarantun. 


Kazalika, shugaban ya ce wannan rage kudin na makarantun, alamu ne Uba ya fara cika alkawaran da ya daukawar alummar jihar lokacin yakin neman zaben sa. 


Mustapha ya kuma yi kira ga mahukunta a kasar nan, da su yi koyi da wannan hangen nesan na gwamna Uba, mussaman don 'ya'yan talakawa su samu damar zuwa makaranta.


Post a Comment

0 Comments