Gwamnan Zamfara Ya Yi Ta'aziyyar Ambasada M.Z Anka
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya miƙa saƙon ta'aziyyar sa ga 'yan uwa, iyalai da sauran al'ummar jihar bisa rasuwar mai faɗa a ji a duk faɗin jihar Zamfara, Ambasada M.Z Anka, wanda Allah ya yi wa rasuwa da safiyar yau Juma'a. 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa Gwamna Lawal ya nuna alhininsa ga wannan babban rashi, wanda ya siffata da kafa mai wiyan cikewa.  

Ya ce, "Wannan rashi na Ambasada M.Z Anka, ba wai iyalin sa ne kawai suka yi rashin ba, rashi ne na dukkan al'ummar jihar Zamfara. 

"Marigayi Anka ya gudanar da rayuwar sa cikin tsari abin koyi, mai gaskiya da hazaƙa. Gudumawar da ya bayar wajen ƙirƙiro da jihar Zamfara, ta isa ta zama shaida ta kasancewar sa mai kishi da neman ci gabam al'ummar sa. 

"A madadin gwamnatin jiha, mu na miƙa saƙon ta'aziyyar mu ga iyalan sa da masarautar Anka. 

"Muna kuma roƙon Allah ya gafarta masa kura-kuran sa, ya sanya shi a Aljannar Firdausi."

Post a Comment

0 Comments