Bunkasa Kasuwannin
Jihar Kaduna
Daga Aliyu Ibrahim
Gwamnatin Jihar Kaduna, karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta bayyana aniyar ta na magance korafe-korafe da kalubalen da ‘yan kasuwa ke fuskanta dangane da shirin rugujewa da sake gina kasuwanni da rabon shaguna da aka yi a zamanin gwamnatin da ta gabata karkashin Mallam Nasir Ahmad El-Rufai.
Taron Jin Ra’ayin ‘Yan Kasuwa da Masu Ruwa da Tsaki
Shugaban Hukumar Kula da Bunkasa Kasuwannin Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Shehu Haruna, ya sanar da wannan kuduri na gwamnati a wani taron ganawa da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci.
Taron ya bai wa shugabannin kungiyoyin ‘yan kasuwa damar bayyana korafe-korafen su game da shirin rugujewa da sake tsarin kasuwanni na gwamnatin baya. Babban korafin ‘yan kasuwa shi ne cewa an ruguje kasuwanni amma har yanzu ba a sake gina su ba, sannan kuma an kasa mamaye shagunan da aka gama ginawa saboda tsadar kudin haya da aka dora musu. ‘Yan kasuwar sun roki gwamnati da ta fito da shirin bayar da tallafin kudi don bunkasa kasuwancinsu, ba tare da bashi ba ko kuma bashi mai saukin ruwa.
Sauran batutuwan da ‘yan kasuwar suka gabatar sun hada da bukatar rage kudin hayar shagunan da aka gina da kuma mayarwa masu shaguna na asali wuraren su.
Alkawarin Gwamnatin Uba Sani
Da yake jawabi, Alhaji Ahmad Shehu Haruna ya tabbatar wa ‘yan kasuwar cewa gwamnatin Jihar Kaduna ba ta da niyyar zaluntar su. Ya kara da cewa zai jagoranci isar da korafe-korafen su ga Gwamna Uba Sani don gaggauta magance su. Ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da su ci gaba da ba gwamnati hadin kai don ta samu damar zartar da kyawawan kudirorinta na bunkasa kasuwanni da harkokin kasuwanci gaba daya a jihar.
Matakan Da Za A Dauka Don Magance Kalubalen
Babban Manajan Sashen Gudanar da Ayyuka na Hukumar Kasuwannin Jihar Kaduna ya baiwa taron tabbacin shirin gwamnati na yin ganawa da kamfanonin da tun farko aka ba su kwangilar sake gina kasuwannin. A cewar sa, wannan matakin zai yi nufin samun ragin kudin hayar sabbin shagunan da ake kuka da shi. Haka kuma, shugaban hukumar kasuwannin zai gudanar da ziyarar gani da ido don ganin yadda al’amura ke gudana a kasuwannin fadin jihar.
Wannan matakin zai nuna kokarin gwamnati na inganta tsarin kasuwanni da walwalar ‘yan kasuwa don samun damar gudanar da sana’o’in su da bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
Korafe-Korafen ‘Yan Kasuwa da Bukatun Su.
Alhaji Shehu Aliyu, shugaban ‘yan kasuwar Kakuri, ya koka game da tsadar kudin hayar sabbin shagunan da aka sake ginawa, inda ya bayyana cewa ‘yan kasuwa ba su da ikon biyan wadannan kudade a halin yanzu. Maimakon haka, ya kamata gwamnati ta duba yadda za ta taimaka musu da tallafin kudi don bunkasa kasuwancinsu, ba tare da bashi ba ko rance mai riba.
Ya ce tsarin da aka kawo na kudin shagunan da ke da fadin kafa tara zuwa tara kan Naira Miliyan Biyu ($2,000,000) zuwa uku ($3,000,000) ya zalunci ‘yan kasuwa.
A nasa bangaren, shugaban ‘yan kasuwar Rigasa, Alhaji Abduljalil Abdullahi Na Mama, ya jaddada bukatar gwamnatin Kaduna ta duba yadda za a tallafawa ‘yan kasuwa da kudin kara karfin jarin su, ganin yadda tsare-tsaren baya, musamman a kan kasuwanni, ya sanya wasu daga cikinsu sun sami karyewar jari, wasu kuma ba su da wata mafita illa su koma kasuwanci a kasashe makwabta.
‘Yan kasuwar sun dage kan bukatar samun tallafin kudi daga gwamnati, ko kananan basussuka kai tsaye zuwa gare su, kamar yadda ake yi wa masu masana’antu da kungiyoyin manoma, la’akari da irin tasirin da za su iya baiwa gwamnati da al’umma a lokacin zabubbuka da kuma samar da habakar harkokin tattalin arziki da cinikayya da zuba jari a fadin Jihar Kaduna
0 Comments