HULDA BA KUNGIYAR KWARARRUN DA YAN KWANGILAR SAKA WUTAR LAN TARKI TA KASA NA DA ALFANU MAI YAWA

  






DAGA IBRAHIM ALIYU, KADUNA

Kulla hulda da Kungiyar kwararrun Injiniyoyi  da Masu Kwangilar kayan lantarki yana tattare da samun dinbim alfanu ga wadanda suka gina sabbin gidaje ko matsugunai. don saka musu kayan lantarfi.

Sabon zababben shugaba reshen kungiyar na Jahar Kaduna Alh. Abdullahi Hassan Wanda aka fi sani da (Dan Asabe NEPA) ya baiyyana haka cikin wata zantawa sa da manema labarai anan Kaduna.

Alh. Dan Asabe NEPA, yace akwai bukatar masu  gina sabbin gidaje su lizimci kula da muhimanci kungiyar mai suna Lincesed Electrical Contractor of Nigeria (LECAN) wajen bukatar sayen Kebul –Kebul da sauran kayan lantarki gidajen su, domin su amfani da shawarwarin kwararru a hidimomin su na sayen kayan lantarki.

Yace haka zai taimaka musu wajen kaucewa yiwuwar samun aukuwar gobara ko tabka hassara ta rayukan da  dukiya, mai yawa sanadiyar rashin samun shawarar kwararru ko amfani da kayan lantarki marasa inganci.

Alh. Dan Asabe NEPA, yace kungiyar ta LECAN ta samu cikakken iko daga kamfanonin wutar lantarki na Kasa na zama tamkar mai shiga tsakanin da kwastomomi da ke sayen kayan wutar lantarki dangane da bukatar  samun shawaara kwararru daga kungiyar a tashin farko daga  masu gida sabbin  gidaje damin magance korafe – korafe da ka iya tasowa na rashin  samun dacewa da kayan wutar lantarki masu inganci.

Y ace kungiyar zata cigaba da wayar da kan al’umma dangane da wadanna al’amura da kuma fahimtar muhimanci hulda da kungiyarta (LECAN)

Bayan kamalla zaben manyan jami’an gudanarwa na kungiyar sai a nan gaba za’a rantsar da su domin cigaba da jan ragamar tafiya da harkokin kungiyar..                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                             

Post a Comment

0 Comments