ALIYU IBRAHIM, KADUNA
Matsalalolin lalacewar hanyoyin mota da tsadar man fetur suna daga cikin abubuwan da kungiyar gamayyar direbobin motocin dakon kaya ta kasa (GDN) take bukatar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta lalubo bakin zare akan su, don saukaka harkokin direbobi da safarar kayayyaki da zirgazirgar ababen hawa, da sassauto da farashin kayayyakin masarufi.
Shugaba kungiyar na shiyar zone E, harila yau shugaban kungiyar reshen jahar Taraba Ambassador Hamisu Gidado Abba Namnai yayi wannan kiran cikin wata zantawa da manema labarai a Kaduna.
Ambassador Abba Namnai, yace wadannan matsalolin na ciwa direbobi tuwo a kwarya, wanda ya sanya kudaden shigar da direbobi ke samu ya ragu matuka tun bayana da gwamnatin tarayya ta aiwatar da Karin kudaden farashin man fetur.
Yace samun ragin Farashin Man fetur zai kawo fa’ida sosai, wajen kyautata sana’oin su da walwalar direbobi da saukaka halin matsin rayuwa ga Al’umma masu karamin karfi da kyautata harkokin sana’o’I da kasuwanci dabam dabam a kasa baki daya.
Shugaban Kungiyar Gamayyar Direcbobin Motocin Dakon Kaya ta Kasa, yace kungiyar tana goyon baya gwamnatin shugaba Bola Tinubu a game da manyan ayyuka shinfida hanyoyin mota masu cin dogon zangon da ta sanya a gaba wadda ta tashi daga sakkwato zuwa Badagry a jahar legas da wadda ta tashi da legas zuwa kalaba jahar kurus – Riba.
Ambassador Abba Namnai yace wadannan muhimman aiyukkan hanyoyi da gwamnati ta shugaban kasa Bola Tinubu da aiyyukan inganta tsaro da harkokin Noma da kyautata zaman lafiya tsakanin Al’umma da gwamnatin jihar Taraba bisa jagorancin Gwamna Agbu Kefas suka sanya a gaba. sun chanchanci Al’ummar Jihar Taraba su mara musu baya domin samun nasarar kudurorinsu na raya cigaban Al’umman.
Yace Akwai Bukatar gwamnatin Tarayya ta gyara Babban hanyar sufirin Motocin Tsakanin Arewa da Kudancin Kasan nan daga Jihar Naijar da bullo da wani shirin samar da tallafin kananan basussuka wa direbobin motocin sufuri, don kara inganta sanao’insu.

0 Comments