
Daga Abdullahi Alhssan Kaduna
Wani Jigo a Jam’iyyar APC kuma wanda ya nemi takarar kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya bayyana nadin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaben Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027 a matsayin “zabi mai kyau kuma mai ma’ana.”
Dr. Abdullahi Shinkafi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a gidansa da ke Samaru, Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Ya ce Shugaba Tinubu ya dauki matakin da ya dace wajen zabar Sanata Yari domin jagorantar wannan muhimmin matsayi na yakin neman zaben.
Ya ce dimbin kwarewar Sanata Yari a harkokin gudanar da zabuka, tafiyar da jam’iyya da kuma hada kan magoya baya daga matakin kasa har zuwa karkara, sun sanya shi cikin mutanen da suka fi dacewa da jagorantar yakin neman zaben.
Dr. Shinkafi ya ce, “Sanata Yari ba bako ba ne wajen cin zabuka. A matsayinsa na tsohon Gwamnan Zamfara na wa’adi biyu kuma tsohon Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya gina kyakkyawan tsarin siyasa. Haka kuma, ya nuna kwarewa wajen tafiyar da harkokin jam’iyya da sasanta rikice-rikice a matsayinsa na babban jigo a APC.”
Ya kara da cewa Sanata Yari na da karfin tattalin arziki, kusanci da al’umma a sassa daban-daban na kasar nan da kuma amincewar jama’a, wadanda ake bukata domin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa mai nasara a dukkan jihohi 36 na Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
A cewar sa “Ya fahimci yadda siyasar Najeriya take. Yana da karfin hali, tsari da kuma amincewar jama’a da za su ba shi damar hada kan al’umma domin samun goyon bayan Shugaba Tinubu. Wannan nadin nasa zai taimaka matuka wajen tabbatar da nasarar APC a zaben 2027, in sha Allah.”
Dr. Sani Shinkafi ya kuma yi kira ga magoya bayan APC da su koma cikin al’ummominsu, su kara kaimi wajen wayar da kan jama’a da kuma neman goyon bayan sake zaben Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaben shekarar 2027.
Ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su mara wa dukkan ‘yan takarar APC baya, ba tare da la’akari da bambance-bambancen da ke tsakaninsu ba, yana mai cewa hadin kan jam’iyya shi ne ginshikin samun nasara a zabe.
Jigon daga jihar zamfara ya tabbatar da cewa APC za ta samu nasara cikin sauki a zaben da ke tafe, musamman ganin irin kwarewar siyasa, basira da kuma amincewar jama’a da Sanata Yari ya samu a sassan Najeriya.

0 Comments