![]() |
| Barista Mahmoud Lawal Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna. (A Tsakiya) |
By Aliyu Ibrahim
Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Barista Mahmoud Lawal, ya bayyana cewa harkar ilimi ta ci gaba da samun fifiko wajen Gwamnatin Jihar Kaduna, inda fannin ya sami kashi 25 cikin dari na kasafin kudin jihar na shekarar 2026.
Barista Lawal ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin Babban Taron Shekara-shekara na Kasa karo na 68 na Kungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Kasa (ANCOPSS) da aka gudanar a Kaduna.
Ya bayyana cewa wannan kaso shi ne mafi tsoka da aka ware wa wani fanni guda daya, wanda ke nuna azamar gwamnati wajen ciyar da harkar ilimi gaba.
Barista Lawal kara da cewa jihar ta dauki matakai na karfafa ilimin sakandare ta hanyar kafa Hukumar Ilimin Sakandare ta Jihar Kaduna (Kaduna State Senior Secondary Education Board) gami da aiwatar da sabon tsarin ilimi na 9-3-4 a cikin jihar.
Dan majalisar ya kuma kara da cewa gwamnati ta inganta jin dadin shugabannin makarantu tare da amincewa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen gudanar da makarantu da kuma bunkasa sakamakon koyo da koyarwa.
Ya yaba wa shugabannin makarantu na Kaduna saboda irin jagorancin da suke nunawa, inda ya bayyana su a matsayin guda daga cikin wadanda suka fi kwarai a fadin kasar.

0 Comments