Rikon Amana: Hanyar Samun Nasara A Duniya Da Lahira – Sheikh Sa’idu Ahmed

 

 

  





FROM ALIYU IBRAHIM

An bayyana bayar da kyakkyawar Kulawa dangane da al’amuran da suka shafi nauyi na rikon amana a matsayin wata hanyar samun daukaka da nasara Ga Dan’ Adam na al’amuransa na duniya da lahira.

Babban Liman Massalin Juma’a na Nagwamatse da ke unguwar Rimi a nan Kaduna, Sheikh Sa’idu Ahmed Abdul’aziz ya baiyyana haka cikin hudubar sa ta ranar Jumma’a a Masallacin.

Babban Limamin na masallacin Juma’a na Nagwamatso Unguwar Rimi Kaduna, yayi bayanin cewa samun dan ‘Adam yana sakaci da rikon amana ke sanadin aikata rashawa, da Abkuwa Fitintinu da Ibtila’I dake shafawar al’umma baki daya.

Ya kara da cewa tsare hakki na rikon amana ya rataya a wuyan kowa, da ya kamata a bayar da kyakkyawar kulawa wajen sauke shi yadda ya dace, dan samun dacewa da falala da kyakyawan sakamakan rashin yin haka kuma babban laifi ne a wajen Allah ubangiji.

Yace alhakin tsare hakkin kulawa da rikon amana, ya fara ne tun daga kan tallakawa da masu shugabanci, da tsakanin ma’aurata, da masu makwataka da juna da sauran abokan mu’amala.

Sheikh Sa’idu Abdulaziz ya kuma yi amfani da lokacin hudubar wajen jadadda ta’aziyar masallacin Nagwamatse ga Iyali da yan’uwa limancin yau da kullum na masallacin sheikh Rufa’I Shehu Ya’u da Allah yayi wa rusuwa a ranar Juma’a inda yayi masa addu’ar Allah yajikansi da samun sakaya da gidan Aljanna wanda yace daukacin jama’arsa ta gudane wajen neman ilimi da karantawa ga al’umma. 



Post a Comment

0 Comments