Sani Sha'aban ya rasa kaddarorin sa bisa taurin bashi



 









Sashen Sheriff da Gudanar da Hukunce-hukuncen Farar Hula na Babbar Kotun Jihar Kaduna ya yi gwanjon wasu kadarori mallakin tsohon ɗan majalisar tarayya, Alhaji Mahmood Sani Sha’aban, sakamakon wata takaddama ta bashi da ta daɗe tana gudana tsakaninsa da ɗan kasuwa Alhaji Umar Faruk Abdullahi, a ranar Litinin, 1 ga Yuni, 2026.


Kadarorin da kotun ta yi gwanjonsu sun haɗa da fili da gine-ginen da ke bayan babban gidan Sha’aban da ke gaban Makarantar Sakandaren Therbow a Zariya, mai Takardar Shaidar Mallaka (C of O) mai lamba KD 3984; da kuma fili da gine-ginen da ke kan Plot No. 3, Churchill Road, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 11226.


Sauran kadarorin sun haɗa da fili da gine-ginen da ke Tulips, mahadar MTD da ke gefen titin Queen Elizabeth, GRA Zaria, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 15052, da kuma kamfanin Mazari Nails Limited da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kano, mai Takardar Shaidar Mallaka mai lamba KD 6246.


Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala gwanjon, Mista Abdullahi Yahaya, SAN, lauyan Umar Faruk Abdullahi ya ce abin da aka gudanar a ranar shi ne gwanjo da sayar da kadarorin wanda ake bin bashi kamar yadda hukuncin Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke Zariya ya tanada.



Ya ƙara da cewa kotun ta ƙwace kadarori guda biyar na wanda ake bin bashin, inda huɗu daga cikinsu suke a Zariya, yayin da ɗaya ke Kano.


“Ya zuwa yanzu mun yi gwanjon kadarorin da ke Zariya, yayin da za a gudanar da gwanjon kadarar da ke Kano a wani lokaci nan gaba,” in ji Yahaya. 



Idan zaa tuna ita wannan shari’ar ta samo asali ne daga wata yarjejeniyar bashi da aka kulla a shekarar 2018 tsakanin Hon. Sani Mahmud Sha’aban (Dan Buran Zazzau) da Alhaji Umar Faruk Abdullahi domin taimaka wa Sha’aban wajen warware wata matsala da ta shafi kama shi da tsare shi a gidan yari a kasar Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), a shekarar 2018.


A ƙarƙashin yarjejeniyar, mai bin bashin ya bai wa Sha’aban rancen Dala miliyan ɗaya ta Amurka (US$1,000,000) da kuma Naira miliyan 11.2 ba tare da ruwa ko karin riba ba, bisa tsarin shari’ar Musulunci. Lauyoyin Sha’aban ne suka tsara kuma suka shaida yarjejeniyar, yayin da ɗansa ya sanya hannu a madadinsa, sa'ilin da shi kan shi Sani Sha'aban din bayan dawowar shi daga gidan yari ya sake sanya hannu don tabbatar da amincewarsa da yarjejeniyar.


Daga bisani, Sha’aban ya biya Dala 290,762 daga cikin bashin dala miliyan ɗaya, da ake bin shi amma daga baya ya ƙi biyan sauran kuɗin da suka rage. Daya daga cikin sharuɗɗan yarjejeniyar ita ce a biya bashin cikin watanni shida kuma da irin kuɗin da aka karɓa.


A ranar 12 ga Fabrairu, 2024, Babbar Kotun Shari’a ta 1 da ke GRA Zaria ta umarci Sani Sha’aban, tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kaduna, da ya biya bashin Dala 709,238 da kuma Naira miliyan 11.2 ga Alhaji Umar Faruk Abdullahi.


Kotun ta kuma bayar da umarnin ƙwace kadarorin Sha’aban da aka jingina a matsayin lamunin tabbatar da bashin.


Sakamakon rashin gamsuwa da hukuncin,.Sani Sha’aban ya garzaya inda ya shigar da ƙorafi mai dalilai takwas a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Jihar Kaduna a ranar 13 ga Fabrairu, 2024.


Ya kuma nemi a dakatar da aiwatar da hukuncin, saidai kuma Babbar Kotun Shari’a ta GRA Zaria ta yi watsi da buƙatar, sannan daga bisani Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a ta Kaduna ma ta yi watsi da ita.


Daga nan ya sake garzayawa zuwa Sashen Ɗaukaka Ƙara na Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke Kaduna, inda shi ma ya sha kaye. A ranar 29 ga Satumba, 2025, kotun ta tabbatar da hukuncin da ƙaramar kotu ta yanke.


Kwafin sahihin hukuncin da wakilinmu ya samu a cikin Shari’a mai lamba KDH/Z/12A/2024 ya nuna cewa kotun ta umarci Sha’aban, da ya biya dukkan kuɗaɗen da kotun ta yanke a cikin Naira da Dala ga Babban Magatakardar Babbar Kotun Jihar Kaduna.


Kwamitin alkalan da Mai Shari’a Bilkisu Mohammed da Mai Shari’a Nana Fatima Mohammed suka jagoranta ya bayyana cewa ana iya aiwatar da hukuncin kuɗi sai dai idan wanda ya shigar da ƙara ya tabbatar da cewa wanda zai karɓi kuɗin ba zai iya mayar da su ba idan ɗaukaka ƙarar ta yi nasara.


Kotun ta ce:


“Babu wani abu a gabanmu da ke nuna cewa wanda ake ƙara ba shi da hali kuma ba zai iya mayar da kuɗin hukuncin ba idan ɗaukaka ƙarar ta yi nasara.”


Alkalan sun ƙara da cewa kotuna ba sa son hana wanda ya yi nasara a shari’a cin moriyar hukuncin da ya samu, amma an bayar da sharadin dakatar da aiwatar da hukuncin ne domin tabbatar da adalci.


Hukuncin ya tabbatar da kiyaye kuɗaɗen da aka yanke yayin da ake ci gaba da aiwatar da matakan karɓar bashin ƙarƙashin kulawar kotu.


A halin yanzu, Umar F. Abdullahi, wanda ya samu hukuncin kotu, ya samu izini daga Babbar Kotun Jihar Kano domin aiwatar da hukuncin da Babbar Kotun Shari’a ta 1, GRA Zaria ta yanke na sayar da kadarorin wanda ake bin bashin.


Kadarar da ke lamba 48, Yusuf Road, kusa da Hadejia Road, Bompai, Kano, na daga cikin kadarorin da aka jinginar domin tabbatar da bashin.


Sashen Sheriff da Gudanar da Hukunce-hukuncen Farar Hula na kotun ya sanya ranar 13 ga Yuni domin gudanar da gwanjon wannan kadara bisa umarnin da Mai Shari’a Faruk Lawan Adamu ya bayar a ranar 4 ga Mayu.


Post a Comment

0 Comments