Daga Abdullahi Alhassan Kaduna
Nadin Sanata Abdul’Aziz Abubakar Yari (Marafan Sokoto) a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC na shekarar 2027, mataki ne mai muhimmanci da ke nuni da shiri mai kyau da haɗin kai na cikin jam’iyya.
A bayyana goyon bayan sa, Dr. Sani Abdullah Shinkafi (Wambai), ya fito da muhimman dalilan da suka sa aka zaɓi Sanata Yari domin jagorantar wannan aiki na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima.
![]() |
| DR. Sani Abdullahi |
Sanata Yari ya gina tarihin shugabanci ne tun daga matakin karkata a Jihar Zamfara inda ya riƙe shugabancin ANPP, har ya zama Ma’aji na Ƙasa, ɗan Majalisar Wakilai, Gwamnan Jihar Zamfara, kuma Sanata a Majalisar Dattawa ta 10. Kasancewarsa ɗa a gidan marigayi Alhaji Yari Abubakar na Masarautar Talatan Mafara, tare da karatunsa na gaba da digiri (Masters) daga Jami’ar Salford, ya ba shi haɗakar tarbiyya ta gargajiya da ilimin zamani na gudanarwa.
Haka zalika, a matsayinsa na ɗaya daga cikin ginshiƙan kafa jam’iyyar APC a Arewacin Najeriya, yana da kyakkyawar dangantaka da masarautu, matasa, mata, da sauran masu ruwa da tsaki a fadin ƙasar.


0 Comments